logo

HAUSA

Taron gwamnonin arewa ya bukaci a gudanar da bincike game da harin bom da dakarun sojin Najeriya suka kai a wani kauye dake jihar Kaduna

2023-12-16 15:06:23 CMG Hausa

Gwamnonin arewacin Najeriya sun yi kiran da a gudanar da bincike tare da biyan diya ga mutanen da suka samu raunika da kuma wadanda suka rasa rayukansu a harin bom da dakarun sojin Najeriya suka kai kauyen Tudun-Biri dake yankin karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna kwanakin baya.

Wannan na daya daga cikin kudurorin da aka tattauna yayin taron gwamnonin arewa 19 da aka gudanar jiya Juma`a 15 ga wata a garin Kaduna.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.//////

 

Gwamnoni wadanda suka bayyana takaicinsu game da faruwar wannan al’amari, sun kuma jaddada aniyar tallafawa wadanda suka jikkata da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu yayin wannan harin da rundunar tsaron kasar ta bayyana a matsayin kuskure.

A lokacin da yake jawabi, shugaban kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya, kuma gwamnan jihar Gombe Alhaji Inuwa Yahaya ya ce, kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa hakki ne da ya rataya a wuyan gwamnati, inda ya yi fatan cewa, gwamnati za ta tsananta bincike a kan al’amarin, ko da yake dai gwamnonin sun yaba bisa yadda gwamnatin tarayya ta yi gaggawar daukar mataki a kan hatsarin.

Haka kuma taron gwamnonin ya kara jaddada bukatar gwamnatin tarayya da ta dauki ma-nagartan matakai da za su shawo kan barazanar ayyukan masu garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci a shiyyar.

Inda suka kara da cewa, zaman lafiya yana tafiya ne tare da ci gaba, a saboda haka wajibi mu shawo kansu gaba daya, muddin ba tsaro ba za a taba samun ci gaba ba, domin ’yan kasuwa na saka jarinsu ne kawai a yanayin da suka tabbatar ba shi da barazana ga albarkatunsu.

“A sakamakon hakan dukkannin gwamnonin arewa 19 za mu ci gaba da  aiki tare wajen maganin wadannan jerin kalubale ta hanyar kyautata hadin gwiwa da hukumomin tsaro, da karfafa ayyukan jami’an tsaron sa kai na jihohi, da shigo da al’umma cikin al’amura tare da sulhunta tsakani da amfani da dabarun fasaha na zamani da sake fasalin dokoki da harkokin gudanarwa haka zalika da toshe kafofin da suke haifar da rashin tsaro”. (Garba Abdullahi Bagwai)