logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta musanta zargin bankin duniya dake nuna cewa har yanzu ba a janye tallafin mai ba a kasar

2023-12-15 09:36:19 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta musanta zargin da bankin duniya ya yi na cewa har yanzu ana ci gaba da biyan kudin tallafin mai a kasar.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na Najeriya Alhaji Mohammed Idris ne ya tabbatar da hakan a ganawarsa da manema labarai a birnin Abuja. Ya ce tun a jawabin rantsuwar kama aiki shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur kuma tuni aka fara ganin tasirinsa.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

A dai ranar Laraba 13 ga wata ne a birnin Abuja, yayin taro kan auna yanayin ci gaban kasa a wannan wata na Disamba, Bankin Duniya ta hannun wani jami’insa Mr Alex Sienaert ya bayyana cewar farashin man fetur a Najeriya har yanzu yana nuna cewa gwamnatin tarayyar na ci gaba da biyan tallafi.

Bankin ya ce, muddin dai an cire tallafin man, to kamata ya yi ’yan Najeriya su rinka sayen mai kan Naira 750 a kan kowane lita guda maimakon Naira 650 da ake sayarwa a wasu sassan kasar.

To amma ministan yada labaran na tarayyar Najeriya ya ce, hasashen Bankin Duniya ko kadan ba haka yake ba, domin kuwa tuni gwamnati ta fara cin gajiya daga rarar da take samu sakamakon cire tallafin man, inda ya tabbatar da cewa, a duk wata asusun tarayya yana tunbatsa daga kudaden da a baya ake kashewa wajen tallafin man.

“Ina tabbatarwa ’yan Najeriya cewa, batun tallafin mai ya tafi bisa la’akari da kudaden da suke shiga asusun tarayya da kuma irin kudaden da yanzu jihohin ke samu, daman dai kowa yana da bukatar a cire wannan tallafi, kawai dai yanzu batun yadda ’yan Najeriya za su amfana da kudaden tallafin shi ne abun muhawara.”

Ko da yake ministan yada labaran na tarayyar Najeriya ya ce, duk da janye tallafin man, amma har yanzu akwai yanayin da gwamnati ke samun damar sanya ido domin tabbatar da ganin al’amuran samar da man a cikin kasa sun tafi yadda ya kamata ta hanyar yin ’yan gyare-gyare a wasu bangarori. (Garba Abdullahi Bagwai)