logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira ga bangarorin Sudan ta Kudu da su samar da yanayin gudanar da zabe

2023-12-15 10:56:48 CMG Hausa

A jiya Alhamis ne wakilin kasar Sin ya yi kira ga bangarori daban daban na kasar Sudan ta kudu da su samar da yanayi mai kyau ga babban zaben da za a gudanar a watan Disamba na shekarar 2024.

Dai Bing, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya bayyana cewa, Sudan ta Kudu ta samu jerin muhimman ci gaba wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka sake farfado da ita, da kafa dokokin zabe, da sake tsara hukumomin gwamnati. Babban zaben da za a shirya gudanarwa a watan Disamba na shekarar 2024 na da matukar muhimmanci ga ci gaban kasar da zaman lafiyarta.

Jami’in ya bayyana wa kwamitin sulhu na MDD cewa, kasar Sin ta yi kira ga dukkan bangarorin Sudan ta Kudu da su sanya moriyar kasar da al’ummarta a gaba, da warware sabanin ra’ayi ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna, ta yadda za a samar da yanayin da za a iya gudanar da babban zaben.  

Ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Sudan ta Kudu, tare da kungiyar tarayyar Afrika, da kungiyar gamayyar shuwagabannin kasashen Gabashin Afirka ta samar da ci gaba, wajen ci gaba da tallafawa harkokin siyasa a Sudan ta Kudu. (Yahaya)