logo

HAUSA

An rufe kamfanin tace ruwa dake Harare sakamakon fari da El Nino ta haddasa

2023-12-06 11:21:44 CMG HAUSA

 

Majalisar birnin Harare, babban birnin kasar Zimbabuwe, ta sanar da rufe wata cibiyar samar da ruwan sha, sakamakon karancin ruwan da ake fuskanta a wuraren adana ruwa, yayin da matsalar fari da El Nino ta haddasa, ta mamaye kasar, inda madatsun ruwa da dama suka kafe.

A ranar Asabar din da ta gabata ne, aka rufe cibiyar tace ruwa ta Yarima Edward, cibiya mafi kankanta daga cikin cibiyoyin sarrafa ruwa biyu dake babban birnin kasar, sakamakon karancin ruwan da ake samu a madatsun ruwa na Harava da Seke.

Bayanai na cewa, galibin yankuna dake wajen kudancin birnin, da suke samun ruwa kai tsaye daga cibiyar, rufewar ta shafe su.

Alkaluma daga ma'aikatar lafiya da kula da yara sun nuna cewa, rufe cibiyar tace ruwa ta Yarima Edward na zuwa ne, a daidai lokacin da birnin ke fama da bullar cutar kwalara, wadda kawo yanzu ta yi sanadin mutuwar mutane 13 a Harare da Chitungwiza.

A cewar hukumar lafiya ta duniya (WHO) yaduwar cutar gudawa, na da nasaba da matsalar ruwa mai tsafta da ma tsaftar muhalli. (Ibrahim Yaya)