logo

HAUSA

An yabawa Sin kan taimakon ilimi ga dalibai masu rauni a Habasha

2023-12-06 11:29:01 CMG Hausa

Kasar Habasha ta yabawa gwamnatin kasar Sin, bisa taimakon da take baiwa mutane msu bukata ta musamman a kasar Habasha.

Wannan na zuwa ne, a yayin wani biki na musamman da aka gudanar jiya Talata, domin kaddamar da wani ginin makarantar Kurame ta Alpha dake Adis Ababa, babban birnin kasar Habasha da kasar Sin ta samar, wanda ya samu halartar manyan jami'an gwamnatin Habasha, da jami'an diflomasiyyar kasar Sin dake Habasha, da wakilai daga kungiyoyin agaji na duniya, da mambobin makarantar.

Tallafin na baya-bayan nan, ya kuma kunshi gudummawar muhimman kayayyakin ilimi da dalibai masu rauni dake makarantar Kurame ta Alpha ke matukar bukata.

A jawabinta, ministar harkokin mata da zamantakewar al'ummar kasar Habasha, Huria Ali, ta yabawa gwamnatin kasar Sin, kamfanoni da kungiyoyin agaji, bisa taimakon da suke ci gaba da bayarwa, don kai wa ga 'yan Habasha dake da rauni.

Ginin makarantar mai sassa daban-daban, wanda kamfanin China Civil Engineering Construction Corporation (CCECC) na kasar Sin ke gudanarwa, zai lakume tsabar kudi har dalar Amurka miliyan 1.5 da gwamnatin kasar Sin ta bayar ga wata kungiya mai zaman kanta, mai suna Rehabilitation International (RI), wadda ta sadaukar da nufin tsugunar da kuma inganta jin dadin yara masu nakasa.(Ibrahim)