logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya bayar da umarnin gudanar da bincike game da harin da sojojin kasar suka kai wani kauye bisa kuskure

2023-12-06 11:23:08 CMG Hausa

Rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da wani hari ta sama a jihar Kaduna da ke arewacin kasar a ranar Lahadin da ta gabata, a yayin wani samame na yaki da ta'addanci, amma ta afkawa wani yankin da jama’a ke zaune bisa kuskure, inda ta kashe fararen hula a kalla 85 tare da jikkata wasu 66..

Mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar (NEMA) Halima Suleiman, ta bayyana a yayin wata hira da gidan telabijin na Channels cewa, hukumar ta samu cikakken bayani daga hukumomin yankin cewa, kawo yanzu an binne gawarwaki 85, yayin da ake ci gaba da bincike a karamar hukumar Igabi.

Wata sanarwa da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar na cewa, rundunar sojin kasar, ta amince da aikata "kuskuren" a wata ganawa da ta yi da jami'an gwamnati ranar Litinin.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin, tare da yin kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Tinubu ya bayyana matukar nadama da alhininsa game da kisan, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, mai tayar da hankali, kuma mai sosa rai. (Ibrahim)