logo

HAUSA

WHO ta bukaci al’ummomi su jagoranci shirye-shiryen fatattakar cutar kanjamau daga Afrika

2023-12-01 11:07:41 CMG Hausa

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce cimma burin fatattakar cutar kanjamau baki daya daga Afrika zuwa shekarar 2030, ya dogara sosai da goyon bayan shirye-shiryen da al’ummomi za su jagoranta.

Daraktar hukumar nahiyar Afrika, Matshidido Moeti ce ta bayyana haka a jiya Alhamis, tana mai cewa damawa da al’ummomi na da matukar muhimmanci ga aikin gano cutar kanjamau da wuri da jinyarta da kula da wadanda suka kamu.

A cewarta, taken ranar a bana na “ Al’ummomi su zama jagora” na da nufin karfafa bukatar amfana daga kuzari da jajircewa da ma kirkire-kirkirensu domin cimma burin kawar da cutar baki daya a nahiyar zuwa shekarar 2030.

An ayyana 1 ga watan Disamban kowace shekara a matsayin ranar yaki da cutar kanjamau da nufin kara wayar da kan jama’a game da cutar da tunawa da wadanda ta hallaka tare da kira ga masu ruwa da tsaki su kara mayar da hankali kan ingantattun hanyoyin kariya da na jinyar cutar. (Fa’iza Mustapha)