logo

HAUSA

An kawo karshen musayar wuta tsakanin jami’an tsaron kasar Guinea Bissau da dakarun soji na musamman

2023-12-01 20:12:35 CMG Hausa

Rahotanni daga kafafen yada labaran Guinea Bissau na cewa, a ranar 1 ga watan Disamba agogon kasar, an yi musayar wuta na tsawon sa’o’i da dama tsakanin dakarun tsaron kasar ta Guinea Bissau da kuma dakarun kasar na musamman. A halin yanzu dai, rundunar soji ta musamman ta kama kwamandan rundunar sojin kasar da kuma wasu jami’an rundunar tsaron gaggawa ta kasar tare da tsare su.

A cewar majiyoyin cikin gida, an kawo karshen luguden wutan da ake yi a babban birnin kasar ta Guinea Bissau, kuma sannu a hankali al’amuran cikin gida na lafawa. Dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) na sintiri a kan tituna. (Yahaya)