logo

HAUSA

An amince da kudurin raya Afirka ta amfani da yanar gizo da bunkasa tattalin arziki

2023-11-30 11:23:30 CMG Hausa

Ministocin kasashen Afirka masu lura da sassan sadarwa da fasahohin sadarwa, sun amince da wani kuduri na ingiza sauye sauye domin cin gajiyar yanar gizo da na’urori masu kwakwalwa a kasashen nahiyar, da bunkasa tattalin arziki da zamantakewar nahiyar, da ma samar da guraben ayyukan yi da inganta rayuwar al’ummun kasashen nahiyar.

An cimma wannan matsaya ne a ranar Talata, yayin kammala taron musamman karo na 5, na jami’an tsare tsare ko STC, game da sadarwa da fasahohin sadarwa a Afirka.

Wata sanarwa da kungiyar tarayyar Afirka wato AU ta fitar game da batun, ta ce ministocin sun sha alwashin jajircewa, wajen goya baya ga dunkulewar fannin raya amfani da yanar gizo ko na’urori masu kwakwalwa, da batun sauyin yanayi, da samar da ababen more rayuwa da makamashi, ta yadda za a kai ga cin cikakkiyar gajiya daga yanar gizo ko na’urori masu kwakwalwa.

Bugu da kari, ministocin sun bayyana aniyar su ta tabbatar da goyon bayan manufar kawo sauyi a Afirka ta hanyar amfani da yanar gizo da na’urori masu kwakwalwa, da aiwatar da manufar a zahiri, a matsayin muhimmin jigon ajandar raya Afirka, ta kungiyar AU nan zuwa shekarar 2063, wanda za su gabatar yayin taron AU na badi. (Saminu Alhassan)