logo

HAUSA

Shugaban Saliyo: An kama jagororin dake da hannu a harin da aka kai barikin soji

2023-11-27 10:24:10 CMG Hausa

Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio ya fada a yammacin jiya cewa, an kama dukkan shugabannin da suka kai hari na baya-bayan nan da aka kai wani babban barikin soji da ke Freetown, babban birnin kasar.

A wani jawabi da ya yiwa ’yan kasa, shugaba Bio ya bayyana cewa, tawagar jami’an tsaro ne suka fatattaki maharan, kuma an dawo da kwanciyar hankali.

Ya ce, mutanen ba wai kawai sun kai hari ne a barikin sojoji dake Wilberforce ba, har ma da wasu wurare da suka hada da cibiyar gyaran hali dake titin Pademba, lamarin da ya kai ga arcewar fursunoni.

Shugaban ya kara da cewa, ana ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro da bincike, kuma gwamnati za ta tabbatar da cewa, an hukunta wadanda suka aikata laifin kamar yadda doka ta tanada. Don haka ya bukaci ’yan kasa su hada kai, don tuntakar kalubalen tsaro dake addabar kasar.

Bayan faruwar lamarin, gwamnatin Saliyo ta sanya dokar hana fita a fadin kasar, inda ta bukaci ’yan kasar da su zauna a gida, amma har yanzu ba a sanar da lokacin da za a kawo karshen dokar ba. (Ibrahim Yaya)