logo

HAUSA

‘Yan ta’adda sun yi garkuwa da mutane kimanin 150 a Najeriya

2023-11-26 16:22:32 CMG HAUSA

 

Mazaunan jihar Zamfara dake arewa maso yammacin kasar Najeriya sun shaidawa manema labarai na Reuters cewa, a daren ran 24 ga wata da agogon wurin, ‘yan ta’adda sun kai hari kan kauyuka 4, inda suka yi garkuwa da mutane a kalla 150, yayin da mutum daya ya mutu. Ya zuwa y anzu, gwamnatin kasar ba ta mayar da martani game da lamarin ba, kuma babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

A cikin ‘yan shekarun nan, ana aikata laifin garkuwa da mutane don samun kudade a arewa maso yammacin kasar. (Amina Xu)