logo

HAUSA

Shugaban Saliyo ya bukaci hadin kan kasar bayan matsalar tsaro da aka samu a barikin sojoji

2023-11-26 19:14:35 CMG Hausa

Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio a yau Lahadi ya bukaci hadin kan ‘yan kasar biyo bayan wani lamarin tsaro da ya faru a barikin sojoji dake Freetown, babban birnin kasar Saliyo.

Wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun yi yunkurin kutsa kai cikin rumbun ajiyar makamai na sojoji da ke barikin Wilberforce da sanyin safiyar Lahadi, a cewar sanarwar da ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a ta fitar.

“Jami’an tsaron mu masu karfin gaske ne sun fatattake su kuma an maido da kwanciyar hankali.” a cewar Bio a wani sako da ya wallafa a shafin X, wanda a da ake kira Twitter.

Gwamnatin Saliyo ta kafa dokar hana fita da dare a fadin kasar biyo bayan lamarin tare da yin kira ga 'yan kasar da su zauna a gida. (Yahaya)