logo

HAUSA

Za a dawo da ’yan Najeriya dake gudun hijira a kasashen Kamaru da Chadi da Janhuriyyar Nijar zuwa garuruwan su

2023-11-24 11:42:13 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce, shirye-shirye sun kan kama wajen fara debo ’yan Najeriya da suke gudun hijira a kasashen Kamaru da Chadi da kuma Jamhuriyyar Nijar zuwa garuruwansu.

Kwamishinan tarayyar a hukumar lura da ’yan gudun hijira da mutanen da suka yi kaura daga gidajensu sakamakon rikice-rikicen cikin gida Alhaji Ahmed Tijjani ne ya tabbatar da hakan ranar Alhamis 23 ga wata a Maiduguri lokacin da ya ziyarci gwamna Babagana Zulum da kuma wasu sansanonin ’yan gudun hijira a jihar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Kwamishinan ya shaidawa manema labarai cewa gwamnati ta kuma amince da rufe raguwar sansanonin ’yan gudun hijira dake Maiduguri nan da watan Janairu na shekarar badi, sannan kuma za a mayar da mutanen da rikici ya daidaita zuwa ainihin gidajensu nan bada jimawa ba.

Ya ce, “Kuna ganin dai yadda muke lura da sansanonin ’yan gudun hijira a nan cikin gida, ko da a lokacin wannan ziyara tamu Borno, mun rarraba masu kayayyakin agajin rayuwa da suka hada da kayan abinci da katifun kwanciya da sauransu domin dai su samu natsuwa, to amma fa ba za mu iya ci gaba da wannan hidima ba, wajibi ne a samu canji, kuma hakan zai yiwu ne kawai ta hanyar rufe wadannan sansanoni gaba daya, amma a madadin hakan ne muka samar da kananan birane ga ’yan gudun hijirar inda a cikin wadannan birane za mu samar da wuraren koyon sana’o’i, inda za a rinka ba su horo na dogaro da kai.”

Alhaji Ahmaed Tijjani ya ce, akwai wadannan birane a shiyyoyi shida na Najeriya, akwai daya a nan Maiduguri, akwai a jihar Zamfara, akwai daya a jahohin Kano da Katsina, sannan kuma akwai a jihar Edo da kuma Jihar Nasarawa. (Garba Abdullahi Bagwai)