logo

HAUSA

Masana Sun Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwa Karkashin BRI Domin Bunkasa Ayyukan Masana’antu A Nahiyar Afrika

2023-11-19 15:43:00 CMG Hausa

Masana sun yi kira da a yi kokarin aiwatar da yarjejeniyar kafa yankin ciniki mara shinge ta nahiyar Afrika AfCFTA, tare da bunkasa hadin gwiwar Sin da Afrika karkashin shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya wato BRI, domin ingiza ci gaba mai dorewa a nahiyar.

An yi wannan kira ne lokacin gabatar da sakamakon wani bincike, a yayin wata zama kan yarjejeniyar yankin ciniki mara shinge ta Afrika AfCFTA da bunkasa ayyukan masana’antu a nahiyar, wanda aka yi jiya Asabar a gefen taron tattauna batutuwan tattalin arzikin Afrika a birnin Addis Ababa na kasar Habasha. Taron mai taken ‘Wajibcin raya ayyukan masana’antu mai dorewa a Afrika,” ya hada masana da bangarori masu zaman kansu da manazarta da matasa.

Wata sanarwar da hukumar kula da tattalin arzikin nahiyar Afrika ta MDD (UNECA) ta fitar jiya, ta ce masanan sun ce aiwatar da kunshin yarjejeniyar, zai matukar bunkasa harkokin cinikayya a nahiyar ba tare da matsi kan sauyin yanayi ba.

Game da shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya da Sin ta gabatar kuwa, Abas Omar, wani mai neman digirin-digirgir kan harkokin tattalin arziki a cibiyar nazarin tattalin arziki da harkokin gudanarwa ta kasar Sin, ya ce shawarar ta kara wa masana’antun nahiyar Afrika daraja, yana mai cewa, duk da cewa, ababen more rayuwa kadai ba su isa bunkasa harkokin masana’antu ba, shawarar na bunkasa samar da ababen more rayuwa a nahiyar domin inganta ayyukan masana’antu. (Fa’iza Mustapha)