logo

HAUSA

Masar za ta tura karin tan 650 na kayan abinci zuwa Gaza

2023-11-15 10:59:23 CMG Hausa

Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi, ya bayar da umarni cewa, kasarsa za ta samarwa zirin Gaza karin tan 650 na kayan abinci.

Sanarwar da fadar shugaban kasar Masar din ta fitar jiya Laraba ta ce, tallafin wani bangare ne na ci gaba da kokarin tallafawa al'ummar Gaza a dukkan matakai

A cewar kungiyar agaji ta Red Crescent ta kasar Masar, ya zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba, kasar Masar ta kai tan 6,944 na kayan abinci, da magunguna, da taimakon jin kai zuwa Gaza, tun lokacin da rikici ya barke tsakanin kungiyar Hamas da Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba.

Ma’aikatar lafiya ta Hamas ta bayyana cewa, rikicin da ake ci gaba da gwabzawa, wanda a halin yanzu ya shiga wata na biyu, ya yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa sama da 11,500. (Ibrahim)