logo

HAUSA

Daurarru 140 ne dake gidan yarin Kano suke jiran a zartar masu da hukuncin kisa

2023-11-13 09:19:49 CMG Hausa

Hukumar lura da gyaran hali a jihar Kano dake arewacin Najeriya ta ce, yanzu haka akwai masu laifi har 140 da suke dakon lokacin da za a zartar masu da hukuncin kisa a jihar.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen makon jiya, jami’in hulda da jama’a na hukumar Malam Musbahu Kofar Nasarawa ya ce, akwai wadanda suka shafe sama da shekara goma da yanke masu hukuncin kisa amma har yanzu ba a kai ga aiwatar da hukuncin ba.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Kakakin hukumar ya ci gaba da cewa, wannan adadi ya kunshi maza da mata, sai dai ya ce babu mutum guda na adadin mutanen da hukuncinsa ya danganci rataya.

Malam Musbahu Kofar Nasarawa ya ce, gwamnonin da suka gabata sun gaza sanya hannu a kan takardar hukuncin kisan, ko kuma na yin sassauci daga hukuncin kisan zuwa daurin rai da rai, inda ya ce, doka ta baiwa gwamna damar yin sassauci ko sallamar mai laifi daga gidajen gyaran hali bisa la’akari da shawarwari na majalissar yiwa fursononi afuwa domin rage cunkoso a gidajen yari.

“Kuma su wadannan da suka samu kansu a hukuncin kisa za ka ga karuwa suke yi ba raguwa ba. Kuma za ka ga yawancinsu akwai masu rashin lafiya ta kwakwalwa da rashin lafiya ta jiki. Kusan wadannan sun taimaka wajen samun cunkoson mutane a irin wadannan gidaje namu. Idan muka kalla cewa su irin wadannan da aka yankewa hukuncin kisa wasunsu za ka ga cewa a tsawon shekarun da suka dauka bayan yanke masu hukunci ba su daukaka karar bama saboda rashin kudi da kuma rashin ilimi cewar bari a daukaka kara wanda mai yiyuwa idan ka daukaka kara za ka samu sauki na wannan hukunci ko a rushe shi ko makamantansu, wannan hakika ya taka muhimmiyar rawa wajen cunkoson irin wadannan mutane da aka yankewa hukuncin kisa a irin wadannan gidaje namu.” (Garba Abdullahi Bagwai)