logo

HAUSA

An fitar da rahoton yadda kamfanonin Sin ke sauke nauyin al’umma a Afrika

2023-11-10 11:34:07 CMG

An fitar da rahoto na shekarar 2023 na yadda kamfanonin Sin dake aiki a Afrika ke sauke nauyin al’umma da ya rataya a wuyansu, a jiya Alhamis a birnin Nairobin Kenya.

Rahoton wanda ya bayyana gudunmuwar da kamfanonin suka bayar a bangaren raya tattalin arziki da zamantakewa da kare muhalli, ya ce tun daga farkon wannan karni, kamfanonin kasar Sin sun gudanar da ayyukan da suka hada da gina sama da kilomita 6,000 na layukan dogo a Afrika. Haka kuma, kamfanonin sun taimaka wajen gina tashoshin jiragen ruwa kusan 20 da manyan tashoshin samar da lantarki 80 da kilomita 6,000 na manyan tituna.

A cewar rahoton, a matsayinta na babbar abokiyar huldar cinikayya da zuba jari ta nahiyar Afrika, Sin ta tura jami’an lafiya kimanin 9,000 zuwa nahiyar, haka kuma ta gabatar da damarmakin horo sama da 100,000, lamarin da ya samar da guraben ayyukan yi sama da miliyan 4.5 karkashin ayyuka daban-daban, da suka hada da shirye-shiryen da suka shafi asibitoci da makarantu da filayen wasanni da kuma aikin gona.

Har ila yau, rahoton ya ce galibin harkokin kasuwanci na Sinawa a Afrika, na mayar da hankali ne kan taimakawa nahiyar kara karfinta na ciyar da kanta gaba da rage talauci da raya nahiyar. (Fa’iza Mustapha)