logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Kebbi ta sanya hannu kan yarjejeniyar kwangila da wani kamfanin kasar Sin

2023-11-08 09:37:18 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Kebbi dake arewacin Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar kwangila da kamfanin China Zhonghao domin ginawa tare da gyara tituna a cikin garin Yawuri.

A lokacin da yake sanya hannu kan daftarin yarjejeniyar a madadin gwamnatin jihar, kwamishinan ayyuka da sufuri injiniya Abdullahi Umar Faruk ya ce, aikin zai lankwame tsabar kudi har sama da naira buliyan 3.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Kwamishinan ayyukan na jihar Kebbi ya ce, aikin kwangilar yana daga cikin manufofin gwamnatin jihar na inganta sha’anin samar da ababen more rayuwa a babban birnin jihar da yankunan manyan masarautun jihar guda 4, da gundumomin ’yan majalissar dattawa guda 3 da kuma hedikwatocin kananan hukumomin jihar guda 21.

Ya ce ko a watan jiya gwamnati ta bayar da kwangilar gyaran tituna a cikin birnin Kebbi da kuma karasa ginin babbar sakatariyar zamani a birnin kan kudi sama da naira buliyan 20.

“A wannan rana ta 6 ga watan Nuwamban shekara ta 2023, bisa umarnin mai girma gwamna ya bayar da izinin a gayawa al’ummar jihar Kebbi gaba daya kuma a yi gaban su, sanya hannu kan yarjejeniya tsakanin jihar Kebbi da babban kamfanin nan na China Zhonghao da za a yi gyaran tituna a birnin Yawuri inda za a gyara tituna da nisan su ya kai kilomita biyar da wani abu, kan kudi naira buliyan uku da miliyan dari takwas da hamsin da hudu da dubu dari biyu da bakwai da kuma naira dari biyu da ashirin da tara da kwabo tara.”

Kamar yadda yarjejeniyar ta nuna za a kammala ayyukan ne cikin watanni 18.

Da yake jawabi a takaice,wakilin kamfanin na China Zhonghao Mr. Wei Merg ya tabbatar da cewa kamfanin zai yi bakin kokarin ganin ya kammala aikin a kan lokacin da aka kayyade. (Garba Abdullahi Bagwai)