logo

HAUSA

Dai Bing: Wanzar da zaman lafiya a yankin Abyei na da matukar muhimmanci

2023-11-07 15:42:27 CMG

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing, ya ce wanzar da zaman lafiya da daidaito a yankin Abyei na da matukar muhimmanci.

Dai Bing wanda ya yi tsokacin a jiya Litinin, ya ce Sin na fatan Sudan za ta kai ga dakatar da bude wuta, ta kuma gaggauta kawo karshen yaki, ta koma teburin shawara da Sudan ta kudu, kana ta sake maido da tsarin siyasa a yankin Abyei.

Har ila yau a dai jiyan, yayin taron kwamitin tsaron MDD da aka yi domin nazarin halin da ake ciki a Abyei, Dai Bing ya bayyana cewa, kasashen duniya sun amince da a warware rikicin Abyei ta hanyar siyasa, wanda hakan ke bukatar hadin kan Sudan da Sudan ta kudu, da kuma goyon baya, da kulawar kwamitin tsaron MDD.

Ya ce cikin tsawon lokaci, yanayin rashin tabbas da ake fama da shi a Sudan, ya yi tasiri ga tsarin siyasar yankin Abyei. Sai dai duk da haka, kasar Sin na jinjinawa, da goyon bayan yunkurin da MDD, da kungiyoyin AU da IGAD ke yi, na ganin an warware takaddamar yankin na Abyei cikin lumana. Har ila yau, Sin na kira ga sauran sassa masu ruwa da tsaki da su samar da tabbacin tsaro na cimma nasarar tsarin tantancewa da sanya ido kan iyakoki.

Daga nan sai Dai Bing ya bayyana fatan kasar Sin, na ganin MDD ta kara fadada tsare tsaren ta na wanzar da zaman lafiya a yankin Abyei, tare da taimakawa al’ummun yankin wajen kyautata yanayin da suke ciki. Bugu da kari, Sin na fatan za a karfafawa daukacin kabilun yankin na Abyei gwiwar daukar matakan kwantar da kura, da zama tare cikin lumana.(Saminu Alhassan)