logo

HAUSA

’Yan ta’adda sun halaka mutane 9 a wajen bikin Maulidi a jihar Katsina

2023-11-07 09:31:52 CMG Hausa

Gungun ’yan ta’adda dauke da bindiga sun kai hari wajen wani bikin Maulidi a kauyen Rugar Kusa dake yankin karamar hukumar Musawa a jihar Katsina inda suka hallaka mutane 9 sannan kuma 18 sun samu raunuka.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a birnin Katsina, ya ce al’amarin ya faru ne da misalin karfe 11 na daren ranar Lahadin makon jiya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Kakakin ’yan sandan na jihar Katsina ya ce, tun farko dai ’yan ta’addan sun yi wa wurin da ake gudanar da Maulidin kawanya ne kafin daga bisani kuma su fara bude masu wuta.

ASP Abubakar Sadiq ya ce, bayan samu rahoton harin ne, jami’an ’yan sanda suka garzaya kauye inda suka fatattaki ’yan bindigan, binciken da aka gudanar dai an gano mutum 9 sun rasu nan take, yayin da 18 da suka hada da mata da kananan yara aka garzaya da su babban asibitin garin Musawa cikin mawuyacin hali, ko da yake daga bisani likitoci sun tabbatar da mutuwar mutane biyu daga cikin mutum 18 da aka kai asibitin.

“A halin yanzu rundunar tana kan bincike, kuma dakarun rundunar sun bazama cikin daji da zummar kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika, sannan idan da wani karin bayani kuma rundunar za ta sanar da jama’a ba tare da wani bata lokaci ba, mai girma kwamashinan ’yan sanda na wannan runduna CP Aliyu Abukar Musa yana mika sakon ta’aziyyarsa ga ’yan uwa da abokan mamatan, kuma yana mai tabbatar masu dacewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin ganin cewa an kamo da kuma gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika.”

A yanzu haka hadin giwar jami’an tsaronsa kai da na hukumomin tsaro a jihar Katsina suna sintiri a kewayen yankin da al’amari ya afku. (Garba Abdullahi Bagwai)