logo

HAUSA

Rundunar tsaro a Najeriya ta musanta batun yunkurin juyin mulki a kasar

2023-11-06 13:53:52 CMG Hausa

 

Babban hafsan tsaron Najeriya Janaral Christopher Musa ya kara tabbatarwa ’yan Najeriya cewa babu wani yunkuri na kifar da gwamnatin farar hula a Najeriya kamar yadda wasu ke yada jita-jita.

Ya tabbatar da hakan ne a Fatakwal dake kudancin kasar yayin bikin kaddamar da wasu ayyuka a runduna ta shida ta sojin Najeriya. Ya ce, sojojin Najeriya a shirye suke a ko da yaushe su kare kimar kasa da martabar demokradiyya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi bagwai ya aiko mana da rahoto.

Babban hafsan tsaron na Najeriya, ya ci gaba da cewa, kamar kowanne dan kishin kasa, sojin Najeriya suna da ra’ayin dorewar mulkin demokradiyya a Najeriya domin ci gaban kasa da hadin kan al’umma.

Janaral Christopher Musa ya ce, dakarun tsaron Najeriya suna da kwarewa sosai ta aiki da sanin ya kamata.

“Ina son tabbatarwa ’yan Najeriya cewa, sojojin Najeriya suna tare da su, kuma za su ci gaba da kare su, haka kuma za mu tsaya tsayin daka wajen kare domkradiyya, a don haka kowa ya cire tsoro ko shakku a zuciyarsa, akwai rahotannin juyin mulki a kasashen Afrika daban daban kamar Burkina Faso da Janhuriyyar Nijar wannan ya janyo tsoro a zukatan wasu, a don haka muna kara jaddadawa ’yan kasa cewa dakarun tsaron Najeriya za su kara jajarcewa wajen tsayawa bisa kare tafarkin demokradiyya.” (Garba Abdullahi Bagwai)