logo

HAUSA

An sake damke tsohon shugaban gwamnatin mulkin sojan Guinea da ya tsere daga gidan kaso

2023-11-05 16:00:56 CMG Hausa

Babban hafsan hafsoshin sojin kasar Guinea Ibrahima Sory Bangoura ya sanar da cewa, an sake damke tsohon shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Moussa Dadis Camara, wanda ya tsere daga gidan yarin Conakry, babban birnin kasar Guinea jiya da safe.

Ibrahima Sory Bangoura, ya tabbatar a cikin wata sanarwa da ya fitar a hukumance cewa, Moussa Dadis Camara, yana cikin koshin lafiya kuma yanzu an mayar da shi babban gidan yarin dake birnin Conakry, yayin da aka sake kame wasu mutane biyu da suka tsere,wato Kanar Moussa Tiegboro Camara da Kanar Blaise Gomou, tare da mayar da su gidan kason

Ya ce, yanzu haka kuma, an dauki dukkan matakan zakulo mutum na karshe da ya arce, wato kwamanda Claude Pivi.

Wata sanarwa da ma'aikatar shari'a ta fitar na cewa, babban mai shigar da kara na kotun daukaka kara da ke birnin Conakry, ya ba da umarnin fara shari'ar manyan laifuka kan dukkan fursunonin hudu da wasu mutane dauke da makamai suka fitar a ranar Asabar daga babban gidan yarin.

Wadannan fursunonin sun hada da Kyaftin Moussa Dadis Camara, tsohon shugaban rikon kwarya, da Kanar Moussa Tiegboro Camara, tsohon minista mai kula da yaki da miyagun laifuka da manyan 'yan bindiga a fadar shugaban kasa, Blaise Gomou, tsohon mamba a kungiyar yaki da miyagun kwayoyi da Kwamanda Claude Pivi, tsohon minista mai kula da harkar tsaron fadar shugaban kasa. (Ibrahim)