logo

HAUSA

UNICEF-Gaza mayar da hankali kan yin rijistar haihuwa yana tauye hakkokin kananan yara da dama a Najeriya

2023-11-05 15:05:30 CMG HAUSA

 

Asusun tallafawa kananan yara na majalissar dinkin duniya UNICEF ya ce, duk da cewa shirin yin rijistar haihuwa na kananan yara ya kankama a Najeriya, amma har yanzu akwai kaso mai yawa na yaran da ba a yi wa rijistar ba.

Babban jami’in asusun mai lura da jihohin Kano, Jigawa da Katsina, Mr. Rahma Rihood Mohammed Farah ne ya bayyana hakan yayin taron karawa juna sani game da gangamin wayar da kai kan batun rijistar haihuwa da aka shiryawa manema labarai da sauran masu ruwa da tsaki a Kano.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.