logo

HAUSA

Wajibi ne Afrika ta tsara sabon tsarin ka’idojin cudanyar al’umma da gwamnatoci domin samun ci gaba mai dorewa

2023-11-04 15:52:20 CMG Hausa

 

Hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD (UNECA), ta yi kira ga nahiyar ta samar da wani sabon tsarin ka’idojin cudanyar al’umma da gwamnatocinsu, domin tabbatar da ci gaba mai dorewa.

Wata sanarwar da UNECA ta fitar, ta ruwaito sabon sakataren zartarwar hukumar Claver Gatete na cewa, wajibi ne a samar da sabon tsarin wanda zai inganta tabbatar da adalci da samar da damarmaki bisa daidaito ga jama’a, domin gaggauta samun ci gaba mai dorewa a nahiyar.

Claver Gatete ya bayyana haka ne yayin taro na baya-bayan nan, na masana da masu tsara dabaru mai taken “Gina Sabon Tsarin Ka’idojin Cudanyar Al’umma da Gwamnatoci a Afrika: Zabubbukan Samun Ci Gaban da Ake Burin Ci”, wanda ya gudana a Addis Ababa, babban birnin Habasha.

Ya kara da cewa, samar da sabon tsarin domin makomar Afrika na bukatar mai da hankali kan abubuwan da za su ingiza cimma muradun ci gaba masu dorewa.

Bugu da kari, ya ce ilimi mai inganci da tsarin koyo da kai, za su ingiza cimma burika da dama, yana mai cewa, rawar da ilimi zai taka wajen gina sabon tsarin ka’idojin cudanyar al’umma da gwamnatocinsu, ta dogara ne da saukin samar da shi da arha, yana mai cewa su ne abubuwan da za su karawa dabarun ilimi inganci da tabbatar da daidaito da tafiya tare da kowa. (Fa’iza Mustapha)