logo

HAUSA

‘Yan kungiyar Boko Haram sun kai hari yankin karamar hukumar Geidam dake jihar Yobe

2023-11-04 15:39:18 CMG Hausa

Gwamantin jihar Yobe dake arewa ta gabashin Najeriya ta tabbatar da cewa, ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari a kauyen Nguro-kayya dake yankin karamar hukumar Geidam a farkon makon da muke ban kwana da shi.

Mai baiwa gwamnan jihar shawara kan al’amuran tsaro Birgediya Janaral Dahiru Abdulsalam mai ritaya ne ya tabbatar da hakan ga taron manema labarai a garin Damaturu, jim kadan da kammala taron gaggawa na kwamatin tsaron jihar da aka gudanar bisa jagorancin gwamnan jihar Mai Mala Buni.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Birgediya janaral Dahiru Abdulsalam mai ritaya ya ce taron kwamatin tsaron ya tabo batutuwa da dama da suka shafi tsaro tare da bujiro da wasu sabbin matakai da za su kara kyautata tsaro a yankin na Geidam da ma sauran sassan jihar ta Yobe baki daya.

“Hakika mun samu rahotannin hare-haren ‘yan Boko Haram a wurare daban daban dake yankin karamar hukumar Geidam, kuma an samu mutane da dama da suka jikkata, amma dai duk da kokarin da jami’an tsaro suke yi a jihar, kwamitin tsaron dake karkashin gwamna Mai Mala Buni yana kira ga jami’an tsaron da su kara jan damara wajen tabbatar da ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.”

A kan jita-jitar da ake yadawa cewa, wai akwai wasu yankuna a yankin karamar hukumar ta Geidam da ‘yan kungiyar Boko Haram ke karbar haraji daga jama’a, mashawarcin gwamnan a kan harkokin tsaro ya ce sam ba gaskiya ba ne, domin kawo yanzu babu wani mutun da ya tabbatar cewa yana biyan ‘yan ta’adda kudade haraji, ko kuma kudin fansa.

Yanzu haka dai an baza jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ‘yan sanda a yankunan karamar hukumar ta Geidam. (Garba Abdullahi Bagwai)