logo

HAUSA

Jihohin dake arewacin Najeriya za su rinka aiki tare wajen lura da kan iyakoki

2023-11-02 09:26:16 CMG Hausa

Hukumar lura da kan iyakoki a tarayyar Najeriya ta bukaci jihohin da suke da makwaftaka da jamhurriyar Nijar da su taimaka mata wajen sanya ido a kan yankunan da suke daf da kan iyaka.

Darakta janaral na hukumar Adamu Adaji ne ya bukaci hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki tare da wasu gwamnonin jihohin arewa maso yamma da arewa maso gabas da aka gudanar a Sokoto. Ya ce wajibi ne a lura sosai saboda wasu bata gari na fakewa da irin wadannan garuruwa wajen lalata kyakkyawan dangantakar dake tsakanin al’umomin kasashen biyu.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Daraktan janaral din ya ce, ganin yadda wadannan jihohi suka fi kusanci da jamhuriyar Nijar, ya sanya yanzu haka hukumar take kara daukar matakai na hadin gwiwa da su domin dakile yaduwar ayyukan ta’addanci da kyautata tsaro da kuma na tattalin arziki a garuruwan da suke da iyaka da Nijar din.

Ya ce, akwai kananan hukumomin dake kan iyakoki wanda suke gudanar da hulda kai tsaye da wasu manyan garuruwa a jamhuriyar Nijar ba tare da sanin hukumomi ba, inda ya ce, lallai ne gwamnonin jihohin su taimakawa hukumar wajen sanya ido.

Daraktan janaral na hukumar lura da kan iyakoki ta tarayyar Najeriya ya tabbatar da cewa, jihohi 7 ne da kananan hukumomi 21 suke amfani da iyaka guda da jamhuriyyar Nijar.

“Muna son jihohin da suke kan iyaka da Nijar ya zama an hada kansu a samu wani dandalin tattaunawa domin tunkarar ’yan uwanmu na Nijar wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kai, wanda zai kawo mana ci gaban kasashenmu guda biyu da kuma kawo sauki wajen rikici da rashin jituwa kana da ayyukan miyagun mutane.”

Wakilai daga jihohin Sakkwato, Kebbi, Zamfara, Katsina, Yobe, Borno da kuma Jigawa ne suka halarci taron, tare da alkawarin bayar da gudummawar da ake bukata wajen samun nasarar manufofin gwamnati a kan sha’anin tsaro a kan iyakoki. Sun kuma bayyana gamsuwarsu bisa matakin gwamnatin tarayyar wajen shigo da su cikin tsarin lura da kan iyakokin. (Garba Abdullahi Bagwai)