logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Nijar ya halarci bikin murnar fara aikin hadin gwiwar Sin da Nijar na hakar man fetur

2023-11-02 14:54:42 CMG Hausa

An gudanar da bikin murnar fara aikin hadin gwiwar Sin da Nijar na hakar man fetur a wurin hakar mai dake Agadem a jiya Laraba. Firaministan Nijer Lamine Zeine ya halarci bikin tare da wasu mambobin majalisar ministocin kasar, kuma jakadan Sin dake kasar Jiang Feng, da babban manajan kamfanin man fetur na Sin dake Nijar Zhou Zuokun da sauran manyan baki sun halarci bikin.

A cikin jawabinsa, jakada Jiang Feng ya bayyana cewa, aikin babban sakamako ne na hadin gwiwar Sin da Nijar, wanda zai kara yawan man fetur da kasar ke hakowa, zai kuma taimakawa Nijar wajen zama kasa mai fitar da tarin albarkatun man fetur. 

Yayin kammala taron kolin hadin gwiwar kasa da kasa karo na uku kan shawarar “ziri daya da hanya daya” wato BRF, bangaren Sin ya yi fatan inganta hadin gwiwa mai amfani tsakaninsa da Nijar, tare da kawo alherai ga al’ummun kasashen biyu.

Firaministan Nijar, da kuma ministan man fetur din kasar sun bayyana cewa, aikin hakar danyen man fetur na Agadem, yana da ma’anar tarihi ga Nijer. Kuma a karkashin hadin gwiwa mai kyau na Sin da Nijar, gwamnatin Nijar za ta inganta gina kasa, da kyautata albarkatu, da kudaden shiga daidai gwargwado, ta yadda hakan zai haifar da babban alheri ga al’ummar Nijar yayin ci gaba. (Safiyah Ma)