logo

HAUSA

‘Yan sanda: ‘Yan Boko Haram sun kashe akalla mutane 40 a jihar Yobe ta Najeriya

2023-11-02 09:52:18 CMG Hausa

Kusan mutane 40 ne suka mutu a jihar Yobe ta Najeriya tsakanin ranakun Litinin zuwa Talata bayan da ‘yan kungiyar Boko Haram suka bude wuta kan mai uwa da wabi da tayar da nakiya a wani kauye, wanda ya kasance babban hari na farko da suka kai jihar ta arewa maso gabashin kasar cikin watanni 18, kamar yadda rundunar 'yan sandan kasar ta bayyana a ranar Laraba.

Rundunar ‘yan sandan ta kara da cewa, ‘yan bindigan sun bude wuta kan mutanen kauye, inda suka kashe akalla mutane 17, sannan kuma a ranar Talatar da ta gabata ne wata nakiya ta tashi, inda ta kashe akalla mutane 20 da ke dawowa daga jana’izar wadanda harin da aka kai a baya ya rutsa da su. (Yahaya)