logo

HAUSA

Tawagar wakilan JKS ta ziyarci kasar Kamaru

2023-11-01 15:25:05 CMG Hausa

Tawagar wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS) karkashin jagorancin daraktan kwamitin ilimi da harkar rubuce-rubuce na cibiyar tarihi da adabi ta JKS Wang Junwei, ta ziyarci kasar Kamaru daga ranar Asabar zuwa Talata.

A yayin ziyarar, tawagar ta gana da mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Theodore Datouo da kuma Jean Nkuete, babban sakataren kwamitin koli na jam'iyyar RDPC mai mulkin kasar Kamaru, inda suka yi karin haske kan hanyar zamanantarwa ta kasar Sin da manufofin kasar Sin zuwa ga Afirka.

Bangarorin biyu sun kuma yi musayar ra'ayi kan aiwatar da muhimmin matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma da kuma zurfafa dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu da kasashen biyu. (Yahaya)