logo

HAUSA

A kalla mutane 17 sun rasu sakamakon hadarin jirgin ruwa a jihar Taraba

2023-10-31 10:07:02 CMG Hausa

Rahotanni daga jihar Taraba dake shiyyar tsakiyar Najeriya, na cewa an tsamo gawawwakin mutane a kalla 17, sakamakon kifewar wani jirgin ruwa da suke ciki a ranar Asabar din karshen makon jiya.

A jiya Litinin, babban jami’in hukumar ba da agajin gaggawa NEMA a jihar ta Taraba Bashir Garga ya ce, an yi nasarar ceto karin wasu mutanen 12 da ransu, ana kuma ci gaba da gudanar da ayyukan ceto a yankin da hadarin ya auku.

Garga ya shaidawa manema labarai cewa, jirgin ruwan na dakon fasinja ya yi hadari ne yana dauke da a kalla mutane 104, ciki har da yara kanana da mata, a kan hanyarsa ta zuwa karamar hukumar Karim Lamido daga wata kasuwar kauye.

Jami’in ya alakanta aukuwar hadarin da mummunan lodi da aka yi wa jirgin ruwan, ya kuma ce suna ci gaba da bincike kan aukuwar lamarin.

Cikin wata sanarwar da ya fitar, gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas, ya bayyana hadarin da mummunan bala’i mai tada hankali, ya kuma yi kira ga masu ba da taimaka ’yan asalin wurin da su kara kaimin aikin da ake yi na ceton wadanda ibtila’in ya rutsa da su. (Saminu Alhassan)