logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Legos ta fara rushe gine-gine da aka yi ba bisa ka’ida ba a yankunan Lekki da Ikoyi

2023-10-31 09:15:02 CMG Hausa

Ma’aikatar muhalli da albarkatun ruwa ta jihar Legos ta ce, ba za ta lamunci yin gine-gine a kan magudanar ruwa ba, da kuma gudanar da harkokin kasuwanci a kan titunan dake birnin.

Kwamashinan ma’aikatar Tokunbo Wahab ne ya bayyana hakan jiya Litinin 30 ga wata lokacin da ya jagoranci aikin rushe wasu gine-gine a yankin Ikoyi.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Tun dai daga makon jiya ne ma’aikatar ta fara aikin rushe gine-ginen da aka yi su a kan magudanan ruwa a yankin Lekki dake jihar.

Kwamashinan muhallin na jihar ta Legos ya ce birnin Legos ba birni ne da ya kamata a bari wasu su rinka lalata ainihin taswirarsa ba, wajibi ne gwamnati ta shigo wajen tabbatar tsaftar birnin yadda ya kamata.

Ya ce, akasari irin wadannan gine-gine su ne suke haifar da yawaitar ambaliyar ruwa a birnin na Legos, sannan kuma mahukunta suna fuskantar kalubale wajen kai dauki a duk lokacin da wata annoba ta afku.

“A safiyar ranar Litinin mun fara aikin rushe wadannan gine-gine domin dai hanyacin jiharmu ta dawo, tun da farko mu tattauna da masu irin wadannan gine-gine inda muka zartar da matsayar cewa, su janye gine-ginensu zuwa tazarar mita 2 ta kowanne bangare wannan shi ne zai rinka ba mu damar yashe magudanan ruwan cikin sauki.”

Mr. Tokunbo Wahab ya bayyana takaicin yadda kalilan ne daga cikin masu irin wadannan gine-gine suka bi umarnin gwamnati wajen kauracewa wuraren da aka bukaci su tashi tun da farko.(Garba Abdullahi Bagwai)