logo

HAUSA

Jam’iyyar SDF mai adawa a Kamaru ta zabi sabon shugaba

2023-10-30 10:54:32 CMG Hausa

Jami’iyyar adawa ta SDF a kasar Kamaru, ya zabi Joshua Osih a matsayin sabon shugabanta, wanda zai rike ragamar ta har tsawon shakaru 5 masu zuwa.

An ayyana mista Osih a matsayin sabon shugaban jam’iyyar ne a jiya Lahadi, bayan ya lashe akasarin kuri’un da aka kada, yayin babban taron zabe na ‘ya’yan jam’iyyar da ya gudana a birnin Yaounde fadar mulkin kasar ta Kamaru.

Da yake tsokaci bayan lashe zaben, mista Osih ya sha alwashin kare ka’idojin jam’iyyar, tare da sauke nauyin dake wuyan sa gwargwadon iko.

Osih mai shekaru 54 a duniya, dan kasuwa ne, kuma mamban majalissar dokokin kasar, ya kuma shiga jam’iyyar SDF a shekarar 1991, kana ya yiwa jam’iyyar takarar shugabancin kasa a shekarar 2018, inda ya zamo na 4 a zaben. Ya maye gurbin marigayi John Fru Ndi, wanda ya mamaye bangaren siyasar adawa a Kamaru cikin sama da shekaru 30. (Saminu Alhassan)