logo

HAUSA

Jagoran SAF ta Sudan ya ce ba za su shiga tattaunawar siyasa a nan gaba ba

2023-10-30 10:32:26 CMG Hausa

Shugaban majalissar rikon kwarya, kuma babban kwamandan sojojin gwamnatin Sudan ko SAF a takaice Abdel Fattah Al-Burhan, ya ce banagaren su ba zai shiga duk wata tattaunawar siyasa da za a gudanar a nan gaba ba, ko shiga tsakani a harkokin da suka shafi gwamnatin rikon kwaryar kasar mai zaman kan ta.

Wata sanarwa da rundunar SAF ta fitar, ta ce Al-Burhan ya yi tsokacin ne a jiya Lahadi, yayin wata ganawa da ya yi da wakilin musamman na kasar Switzerland a yankin kahon Afirka Sylvain Astier a Port Sudan, fadar mulkin jihar Red Sea dake gabashin kasar.

Yayin ganawar, an nazarci batun muhimmancin kafa gwamnati mai zaman kan ta, wadda za ta yi jagoranci na rikon kwarya, gabannin gudanar da babban zabe a Sudan.

Kaza lika sanarwa ta ce an nazarci matakai daban daban na cikin gida da na waje da ake dauka domin kawo karshen yaki a Sudan, da yanayin jin kai a kasar, da hanyoyin kai agajin jin kai ga masu bukata a kasar.

Cikin wata sanarwa da mataimakin babban sakataren MDD mai lura da harkokin jin kai Martin Griffiths ya fitar a ranar 15 ga watan Oktoba, jami’in ya ce tun daga ranar 15 ga watan Afirilun bana, ake dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnatin Sudan ko SAF, da dakarun ko ta kwana na RSF a birnin Khartoum da wasu sassan kasar, lamarin da ya haddasa kisan mutane kimanin 9,000, tare da tilastawa sama da wasu mutanen miliyan 5.6 barin muhallansu, baya ga mutane miliyan 25 da yakin ya jefa cikin yanayi na bukatar agajin jin kai.  (Saminu Alhassan)