logo

HAUSA

Matatar mai ta Kaduna za ta fara aiki a karshen watan Disamban badi

2023-10-29 16:01:11 CMG Hausa

Karamin minista a ma’aikatar man fetur na tarayyar Najeriya Sanator Heineken Lok-pobiri ya ce, an fara daukar matakan farfado da ayyukan matatar man Kaduna, kuma akwai fatan cewa cikin watan Disamban shekara ta 2024, za ta dawo aiki gadan-gadan.

Ministan ya tabbatar da hakan ne lokacin da ya kai ziyarar aiki matatar jiya Asabar 28 ga wata domin duba mastayin da aikin gyaran ke ciki.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Karamin ministan wanda yake tare da babban shugaban gungun kamfanin mai na NNPC Malam Mele Kyari da sauran shugabannin kamfanin a yayin ziyarar, ya ce yana rangadin daukacin matatun man dake Najeriya ne a kokarin da gwamnati ke yi wajen tabbatar da ganin kafin wani lokaci mai tsawo Najeriya ta daina shigo da tattaccen mai daga waje kamar yadda shugaban kasa ya yi alkawari.

Sanata Heineken ya ce bisa la’akari da yadda aikin ke gudana, yana da kwarin gwiwar cewa matatar man ta Kaduna za ta iya dawowa aiki a wa’adin shekara guda da aka diba.

“Za mu yi duk abun da ya kamata wajen taimakawa kamfanin mai na NNPC domin ganin cewa mun biyawa ‘yan Najeriya burin su, gyaran matatun man yana da mahimmanci sosai ga dorewar tattalin arzikin mu.”

A lokacin da yake jawabi, babban shugaban gungun kamfanin mai na kasa Malam Mele kyari ya shaidawa ministan cewa, tuni kamfanin da zai yi kwangilar gyaran ya samar da dukkan kayayyakin aiki a matatar kuma ma har ya fara aikin gyaran.

“Muna da yakinin cewa za mu sami kudaden da suka kamata wajen gudanar da wannan aiki har zuwa kammaluwar sa, wanda daga bisani zai kara sanya farin ciki a zukatan ‘yan Najeriya.”

Idan dai matatar man ta Kaduna ta fara aiki, ana sa ran za ta rinka tace ganga dubu 60 a kullum.(Garba Abdullahi Bagwai)