logo

HAUSA

AU ta yi kira da a karfafa tattalin arzikin mata domin yakar matsalar wariyar jinsi

2023-10-29 16:06:39 CMG Hausa

Kungiyar Tarayyar Afrika (AU), ta nanata bukatar kara kokarin bunkasa tattalin arzikin mata domin kawo karshen matsalar wariyar jinsi da ake nunawa mata da ‘yan mata a nahiyar.

Wata sanarwar da AU ta fitar a ranar Jumma’a, ta ce samar da damrmakin samun hidimomin kudi, mataki ne da zai kai ga tabbatar da daidaiton jinsi da karfafawa mata a fannin tattalin arziki da kuma kawo karshen cin zarafinsu.

A cewar AU, cin zarafin mata da ‘yan mata take hakkokinsu ne, kuma babbar matsalar lafiyar al’umma ce dake tarwatsa rayuwar daidaikun mutane.

Ta kara da cewa, bisa la’akari da yanayin zamantakewa da shari’a da sauye-sauyen da ake bukata wajen samar da muhallin inganta daidaiton jinsi da damarmakin samun hidimomin kudi, shigar da maza cikin dabaru da matakan kandagarki da kawo karshen cin zarafin mata, na da muhimmanci matuka.

Daya daga cikin burikan raya nahiyar na shekaru 50 na AU, wato ajandar da ake son cimmawa zuwa shekarar 2063 shi ne, samar da nahiyar da mutane ne za su ingiza ci gabanta, wadda ke dogaro da karfin al’ummarta, musammam mata da matasa, tare da bayar da kulawa ga yara. (Fa’iza Mustapha)