logo

HAUSA

Kotun kolin Nijeriya ta tabbatar da nasarar zaben shugaban kasar

2023-10-27 09:49:51 CMG Hausa

Kotun koli a Nijeriya ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe, wadda a baya ta tabbatar da nasarar shugaba Bola Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a watan Fabrerun bana, a kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika.

Dukkanin alkalan kotun 7 ne suka tabbatar da hukuncin, wanda ya zo bayan shafe watanni ana shari’a. Babbar jami’iyyar adawa a kasar wato PDP da Jam’iyyar Labor (LP) ne suka shigar da karar, suna zargin an tabka kura-kurai yayin gudanar da zaben.

Kotun kolin dai ta kori karar da jam’iyyun adawar suka shigar, inda ta yanke hukunci cewa, Tinubu shi ne halaltaccen shugaban da aka zaba a kasar, bisa la’akari da cewa, ya cike dukkanin ka’idojin da doka ta gindaya. (Fa’iza Mustapha)