logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga jamhuriyar Afrika ta tsakiya da ta zabi hanyar da ta dace da yanayinta

2023-10-27 14:35:40 CMG HAUSA

Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD Dai Bing, ya ce dole ne kasashen duniya su mutunta ikon mulkin kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, da goya mata baya wajen zabar hanyar da ta dace da yanayinta.

Dai Bing ya bayyana haka ne a gun taron tattaunawa kan batun jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da kwamitin sulhu na MDD ya yi a jiya, inda ya kara da cewa, ana ta samun ci gaba wajen shimfida zaman lafiya a kasar a ‘yan kwanakin nan. Kuma Sin na farin ciki sosai da ganin yadda kasar ta samu ci gaba a fannin tarwatsa masu makamai da yiwa hukumomin tsaro kwaskwarima da wanzar da zaman lafiya da samun sulhu tsakanin wurare daban-daban da sauransu. Ya ce daga cikin kungiyoyi masu dauke da makamai 14 da suka sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, 9 sun tarwatsa kansu, matakin da ya taka rawa wajen shimfida zaman lafiya da gudanar da zabe a wurare daban-daban.

Dai Bing ya yi nuni da cewa, Sin na maraba da matakin da kwamitin ya dauka a watan Yuni, wanda ya kyautata manufar hana sufurin makamai a kasar. A sa’i daya kuma, gwamnatin kasar na fatan za a soke duk takunkuman da aka kakaba mata. Ya kamata kwamitin sulhu ya saurari bukatun kasar da kuma dora muhimamanci kan abubuwan da kasar ke mai da hankali a kai, da ci gaba da kyautata matakan takunkuman da aka sanyawa kasar, wadanda ke kayyade aikin tsaron kasar. (Amina Xu)