logo

HAUSA

Shugaba Tinubu ya amince da fitar da Naira biliyan 18 domin biyan hakkokin sojojin da suka mutu a fagen fama

2023-10-26 09:42:03 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da fitar da Naira biliyan 18 domin biyan iyalan tsoffin sojojin da suka rasu da kuma wadanda suka bar aiki.

Ya tabbatar da hakan ne jiya Laraba 25 ga wata lokacin da yake kaddamar da asusun tunawa da tsoffin sojoji na shekara ta 2024 a fadarsa dake birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Shugaban ya kuma bayar da tabbacin cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da bayar da goyon baya ga rundunar sojojin kasar tare kuma da sauran hukumomin tsaro ta hanyar sake fasalta tsarin ayyukansu ta yadda za su kara samun karsashin tabbatar da kasa mai cike da aminci da walwala ga duk wanda yake zaune a cikinta.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce, ganin dinbun bashin da tsoffin sojojin suke bi ya sanya ya amince da fitar da wadannan kudade a matsayin hakki ga iyalan ’yan mazan jiyan da suka riga mu gidan gaskiya tare kuma da sauran dakarun da suka yi ritaya, wannan kamar yadda ya fada kadan ne daga cikin tagomashin da gwamnatinsa ta tsara yi wa dakarun da iyalansu bisa gamsuwa da hidimar da suka yi wa kasa a baya.

Shugaban na tarayyar Najeriya ya ja hankalin ’yan kasuwa da su rinka saukakawa tsoffin sojojin da suka bar aiki a duk lokacin da suka je kasuwa domin yin sayyaya.

Bayan kaddamar da asusun shugaban na tarayyar Najeriya ya kuma yi kira ga sauran al’ummar kasa kamar haka.

“Ina kira ga kowa da kowa da a taimaka wajen bayar da gudummawa ga wannan asusu domin taimakawa jaruman sojojinmu da suka yi ritaya tare kuma da iyalan sojin da suka rasa rayukansu, da wannan kira ne nake farin cikin kaddamar da asusun tunawa da tsoffin ’yan mazan jiya na shekara ta 2024.” (Garba Abdullahi Bagwai)