logo

HAUSA

Za a yi wa yara ’yan mata sama da miliyan 7 allurar riga-kafin ciwon dajin bakin mahaifa a Najeriya

2023-10-25 09:31:21 CMG HAUSA

 

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da shirin allurar riga-kafin ciwon dajin bakin mahaifa, wanda aka kiyasta za a yi wa yara mata miliyan 7.7

Da yake kaddamar da shirin a babban dakin taro dake fadar shugaban kasa, ministan lafiya Dr Muhammad Ali Pate ya ce, yara mata da shekarunsu bai gaza 9 zuwa 18 ba, za a yi musu allura guda daya, wadda za ta kare su daga kamuwa daga mataki na 16 da 18 na kwayoyin cutar dake zama sanadin kaso 70 na samuwar ciwon dajin ga mata.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.