logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta yi alkawarin samar da wadatattun kudaden musaya ga masu saka jari

2023-10-24 09:40:30 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ’yan kasuwar kasar cewa, shirye-shirye sun yi nisa wajen kyautata sha’anin samar da kudaden waje domin bunkasuwar hada-hadar kasuwancinsu.

Shugaban ya tabbatar da hakan ne jiya Litinin 23 ga wata a birnin Abuja lokacin da yake jawabi wajen babban taron wakilan kungiyar tattalin arzikin kasa karo na 29.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce yana da kwarin gwiwar cewa za a iya cimma burin samar da dala tiriliyon 3 domin gudanar da ayyukan raya kasa cikin shekaru 10 ta hanyar yin hadin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu.

Sai dai kuma ya ce, wajibi ne masu zuba jari su ma su ba da tasu gudumawar wajen inganta sha’anin kudaden musaya na kasashen ketare.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kara da cewa, gwamnati za ta bi dukkan sharuddan da aka gindaya wajen samar da kudaden musaya ga ayyukan kwangiloli mallakin gwamnati, kuma tuni ma aka samar da tsarin da zai tabbatar da cika wadannan sharuda.

Shugaban tarayyar Najeriya ya ce, yana sane da kalubalen da ’yan kasuwa ke cin karo da su a kasuwar hada-hadar kudaden waje, inda ya tabbatar musu da cewa, shirin samar da karin wadatattun kudaden waje da gwamnati ke kokari a kai zai taimaka wajen samar da daidaito a kasuwar.

A karshen jawabin na shugaban kasa kafin kaddamar da taron, ya yi kira ga mambobin kungiyar babban taron tattalin arziki na kasa cewa,

“A yau ina kira a gare ku, a mastayinku na daya daga cikin fitattun kungiyoyi masu zaman kansu da suke bayar da shawarwari a game da wasu manufofin ci gaba, da ku ninka a kan abubuwan da kuka gudanar a baya, ku kara bijiro da wasu ra’ayoyi, ta amfani da kwarewarku ta jagoranci tare kuma fitowa da dukiyoyinku domin mu taru mu samar da kyakkyawar makoma ga kasa a nan gaba. A yanzu ina farin cikin kaddamar da wannan babban taron tattalin arzikin kasa karo na 29.”

(Garba Abdullahi Bagwai)