logo

HAUSA

Gwamantin jihar Katsina zata saka kafar wando guda da duk basaraken da yake taimakawa ’yan ta’adda

2023-10-22 16:12:36 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Katsina dake arewacin Najeriya tayi barazanar daukar mataki mai tsauri ga duk wani jami`in gwamanti ko basaraken da aka samu yana taimakawa `yan ta`adda wajen gudanar da munmunan aikin su a jihar.

Gwamnan jihar Dr. Dikko Radda ne ya bayyana hakan ga wani taron manema labarai a birnin Abuja, yace yaki da ta`addanci babban jihadin kare rayuwar duk wani dan kishin kasa ne daga barazanar makiya cigaban Najeriya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. ######

Gwamnan na jihar ta Katsina yace a matsayin sarakuna na iyayen kasa ba daidai ba ne a same su da hannu wajen taimakawa duk wani mutum ko kungiyar da bata nufin al`umma da alheri.

Yace a baya an sha samun rahotanni dake nuna hannun wasu shugabanni da hannu wajen taimakawa `yan ta`adda a jihar, inda yace yanzu gwamnatin sa ba zata lamunci hakan ba.

Dr Dikko Radda ya tabbatar da cewa a halin yanzu akwai wasu sarakuna a jihar da jami`an tsaro ke kan binciken su saboda samun su da mu`amulla da `yan ta`adda.

Gwamnan ya ce tun lokacin da ya kasance gwamnan jihar, babu ranar da ba ya samun rahoton an yi garkuwa da mutane ko kuma kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

A kan shawarwarin da wasu ke bayarwa kuwa na yin zaman sulhu da `yan ta`adda, gwamnan na jihar Katsina yace ba shi da niyyar yin hakan ko kadan.

“ Na sha fada cewa ba zan taba yin sulhu da `yan ta`adda ba, yin sulhu da `yan ta`adda ba ya cikin tsarina, sai dai wannan ba zai hana idan `yan ta`addan sun fito da kan su sun ajaye makamansu tare da mika wuya, za mu iya karbar su mu shigar da su cikin al`ummah, amma ba zan taba zuwa ina rokon su ba”.(Garba Abdullahi Bagwai )