logo

HAUSA

Masana sun yi kira da a ingiza samar da tsarin 5G a Afrika domin bunkasa ci gaban tattalin arziki

2023-10-20 13:43:11 CMG Hausa

Masana fasahar sadarwa da suka halarci taron baje kolin fasahohin sadarwar tafi da gidanka na duniya na shekarar 2023, sun ce kasashen Afrika na bukatar karfafawa da gaggauta kokarinsu na samar da tsarin sadarwar 5G a fadin nahiyar domin farfado da ayyukan masana’antu da inganta hade yankuna da kuma bunkasa tattalin arziki.

Taron wanda ya gudana a Kigali babban birnin kasar Rwanda, daga ranar 17 zuwa 19 ga wata, ya hallara wakilai sama da 2,500, cikinsu har da shugabannin siyasa da jami’an gwamnatoci da masana da wakilai daga MDD da AU da gomman kamfanonin fasaha da kananan kamfanoni da sauransu, daga nahiyar Afrika da ma sauran sassan duniya.

Amir Abdelazim, masani kuma mai hannun jari a kamfanin Detecon Consulting, ya ce ana sa ran samar da sadarwar 5G zai bayar da gudunmuwa ga ci gaban nahiyar Afrika ta hanyar samar da guraben aikin yi da inganta kudin shiga. Ya ce karfin tattalin arzikin 5G da na’urorin dake amfani da shi ya zarce duk wasu fasahohi da suka zo kafin shi a fannin fasahar sadarwa.

Bisa rahoton tattalin arzikin sadarwar tafi da gidanka na Afrika da kungiyar kamfanonin sadarwa ta duniya ta fitar, karfin tsarin 5G na karuwa a Afrika. Sai dai, yanzu an fi mayar da hankali wajen samar da shi a birane da yankunan masana’antu, inda aka fi bukatarsa. (Fa’iza Mustapha)