logo

HAUSA

Sojoji masu rike da madafun iko a Nijar sun zargi Bazoum da yunkurin tserewa daga kasar

2023-10-20 21:03:26 CMG Hausa

Sojoji masu rike da madafun iko a janhuriyar Nijar, sun zargi hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum da yunkurin tserewa daga kasar.

Gwamnatin sojin wadda ta fitar da sanarwa da safiyar jiya Alhamis, ta ce Mohamed Bazoum tare da iyalan sa, da masu dafa masa abinci su 2, da wasu jami’an tsaro su 2, sun yi yunkurin ficewa daga kasar daga wurin da ake tsare da shi.

To sai dai kuma, sojojin sun ce sun yi nasarar dakile yunkurin tserewar shugaban tare da wadanda ke tare da shi, an kuma damke dukkanin su.

Wasu kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, lauyan Bazum ya musanta aukuwar lamarin, yana mai matukar bayyana adawa da bayanan da gwamnatin ta fitar.   (Saminu Alhassan)