logo

HAUSA

An kaddamar da kwamitin samar da jami’an tsaron musamman a jihar Sokoto

2023-10-19 09:05:08 CMG Hausa

Dubban matasa ne ake sa ran za su kasance cikin rundunar tsaron musamman da gwamnatin jihar Sokoto za ta kirkira nan ba da jimawa, da zummar tabbatar da dauwamammen zaman lafiya a fadin jihar baki daya.

Gwamnan jihar Alhaji Ahmed Aliyu ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake kaddamar da kwamitin da zai lura da aikin tantance matasan tare da fito da tsarin yadda ayyukan rundunar zai kasance bisa bin ka’idojin tsaro a Najeriya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Gwamna Ahmed Aliyu ya ce, yana daga cikin aikin kwamitin wanda yake karkashin jagorancin Kanal Garba Moi mai ritaya, fito da shawarwari a kan yadda za a dauka da baiwa matasan horo, tare kuma da wayar da kan al’ummar jihar a kan tsarin ayyukan jami’an tsaron na musamman.

“Wannan shiri da aka kaddamar a yau, shiri ne wanda mu gwamnonin da abin ya fi shafawa muka yi kudurin cewa, za mu yi wannan runduna mu tabbatar da cewa mun yi amfani da jama’armu da wasu kungiyoyi, mun kare al’ummarmu wato dukiyarsu da kuma rayukansu. Abin da nake nufi a nan, idan aka samu tsaro a Zamfara wadannan ’yan ta’adda za su gudu su je Sokoto, idan aka samu kariya a Sokoto za su koma Kebbi, idan aka kore su daga Kebbi suna iya komawa Niger, idan aka taba su za su iya zuwa Kaduna, idan aka tunkare su a can za su iya shiga Kano ko Katsina, a sabo da haka ne muka yi shiri kuma kowanenmu ya dau damara da yardar Ubangiji na yaki da wadannan mutane marasa tausayi wadanda ba su da imani a zukatansu.”

Ya bukaci ’yan kwamitin da su kiyaye sosai wajen tantance matasan da za su shiga cikin rundunar ta hanyar bin tarihin rayuwarsu ta amfani da ra’ayoyin masu unguwanni, dagatai da malaman addini, wannan zai hana shigo da bara gurbi a aikin tabbatar da tsaron.

Kwamitin dai yana da wakilci daga dukkannin hukumomin tsaro dake aiki a jihar, don bayar da damar fito da gamsasshen rahoto da zai tafi daidai da manufar tsaro ta kasa. (Garba Abdullahi Bagwai)