logo

HAUSA

CNSP ya sanar da kaddamar da asusun zumunci domin fuskantar takunkumin CEDEAO

2023-10-17 10:30:43 CMG Hausa

Bayan sanarwar gyaren kasafin kudi da ya ragu da kashi 40 cikin 100, ta gwamnatin Nijar a ranar 8 ga watan Oktoban shekarar 2023, kwamitin ceton kasa na CNSP ya kaddamar da wani asusun zumunci domin kiyaye tsaron kasa. 

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya duba wannan batu, ga kuma rahoton da ya turo mana.

A cikin wannan sanarwa, sojojin dake mulki bayan juyin mulkin watan Julin da ya gabata, sun bayyana cewa za su yi wani gagarumin aikin neman kudi, ta hanyar gudunmawar kamfanoni, man fetur, ’yan Nijar dake ketare, da kuma daga bangarori daban daban.

Aikin wannan asusun zumunci ya shafi fidda wani karamin kaso daga man fetur, daga kudaden da kamfanonin sadarwa suke samu masu lasisin aiki a Nijar. Da kuma wasu sauran hanyoyin da suka samu amincewa daga al’ummar kasa, domin karbar gudunmawar ’yan kasa, su kasance ma’aikatan gwamnati ko masu zaman kansu.  

Ta haka ne, za’a rika fidda dala biyu na Sefa ga kowane tikitin mota ko tikitin hanya, da fidda jika guda ga kowane tikitin jirgi, haka su ma masu masana’antu, kungiyoyi masu zaman kansu da kungiyoyin ci gaba za su ba da tasu gudummawa.

Haka zalika kuma kwamitin ceton kasa na CNSP ya yi kira ga ’yan Nijar dake kasashen waje da su kawo tasu gudunmawa, kuma tuni wadannan ’yan Nijar da ke ketare sun fara amsa wannan kira na sabbin hukumomin Nijar, inda misali ’yan Nijar dake Togo suka bada miliyan 100 na sefa, haka su ma ’yan Nijar dake Dubai suka ba da miliyan 10 na sefa. 

Zuwa wannan lokaci ’yan Nijar da dama ne suke ci gaba da ba da gudunmawarsu bisa burin taimakawa gwamnatin rikon kwarya tafiyar da aikin da aka dora masa na aza Nijar bisa turba mai kyau da za ta sanya ’yan Nijar kan makoma mai haske, kamar yadda mambobin kwamitin ceton kasa a karkashin jagorancin shugaban kasa Abdourahamane Tchiani suka dauki alwashi.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.