logo

HAUSA

Za'a gina karin sabbin makarantun 'yan mata a jihar Kano dake arewacin Najeriya

2023-10-17 10:45:53 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya ta sha alwashin kawo karshen matsalar rashin karatun ’ya’ya mata a jihar, tare kuma da maganin halayyar wasu iyaye na cire ’ya’yan su daga makarantu ba tare da sun kammala ba.

Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya tabbatar da hakan jiya Litinin lokacin da ya kaddamar da rabon kayan karatu na miliyoyin Naira ga daliban makarantun firamare da na sakandiren dake jihar, ya ce samar da karin makarantun zai cike ratar da aka yi wa jihar Kano a bangaren ilimi.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Gwamnan jihar ta Kano ya ce, jihohin arewa na fuskantar kalubale da dama ta fuskar ilimin yara, inda kowace shekara mizanin adadin daliban da ya kamata a saka a makarantun firamare ke kara raguwa sosai, lamarin da yake da nasaba da talauci da rashin fadarkarwa tare kuma da matsalolin tashe-tashen hankula da ya addabi wasu jihohin dake shiyyar.

Ya ce, miliyoyin Naira gwamnati ta kashe wajen sayo littattafan rubutu da karatu, da kayayyakin sakawa wato uniform ga daliban firamare da jakunan saka littattafai domin dai samar da natsuwa ga dalibai.

“Wannan rana ita ce ranar da muka lakabawa suna Ranar harkar ilimi a jihar Kano domin rana ce da Allah ya ara mana, ya ba mu iko muke cika alkawurukan da muka yi na inganta harkar ilimi ga ’ya’yanmu da jikokinmu a wannan jiha. Wannan rana ce da muka kaddamar da rarraba kayan karatu da karantawa ga kananan yara na firamare da kuma manyan makarantunmu na sakandare da suke fadin wannan jiha.”  (Garba Abdullahi Bagwai)