logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su agazawa bunkasuwar Afirka

2023-10-17 10:52:43 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Dai Bing, ya bayyana a cikin jawabin da ya gabatar yayin taron kolin MDD game da batun bunkasuwar Afirka da zaman lafiya, cewar tallafawa ci gaban Afirka nauyi ne na bai daya na kasashen duniya baki daya.

Dai ya ce, kamata ya yi kasashen duniya su fahimci hakikanin halin da ake ciki da bukatun musamman na kasashen Afirka, da mutunta zabin kasashen Afirka masu cin gashin kansu na hanyoyin samun bunkasuwa da ya dace da yanayin kasashensu, da ba su taimakon da ya dace. 

Na farko, tallafawa Afirka wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Na biyu, taimakawa kasashen Afirka su shawo kan kalubalen samun kudaden raya kasa. Na uku, adawa da tasirin mulkin mallaka, da duk wani nau'i na mulkin danniya, da nuna adawa da kakkaba takunkumi maras dacewa na kashin kai kan wasu kasashen Afirka, da kara wakilci da muryar kasashen Afirka a harkokin kasa da kasa da gudanar da harkokin duniya. Na hudu kuma na karshe, shi ne tallafawa kasashen Afirka wajen inganta kwarewarsu. (Ibrahim Yaya)