logo

HAUSA

Za a fara amfani da totuwar Marasa da bawon Shinkafa a matsayin makamashin girki a Najeriya

2023-10-16 09:10:24 CMG Hausa

 

An fara baiwa mata horon dabarun sarrafa totuwar Marasa da bawon Shinkafa da Ciyayi zuwa makamashin girki a tarayyar Najeriya, a wani mataki na magance matsalolin dumamar yanayi.

Kungiyar alkinta muhalli da bayar horon dogaro da kai ga mata Development Exchange Center DEC tare da hadin gwiwa da kungiyar wayar da kan matan karkara kan sha’anin ci gaban rayuwa Community Advocacy for Rural Development CARD su ne suka dauki ragamar bayar da horon ga mata 20 a garin Baraza dake yankin karamar hukumar Dass a jihar Bauchi.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Mrs Habibu Ajuppo ita ce babbar daraktan kungiyar CARD da ta jagoranci shirya taron ilimintarwa ga matan garin na Baraza.

“Muna aiki ne muna taimakawa al’umma karkashin yaki da sauyin yanayi, mun ga yadda yanayi yake canjawa kuma mun lura cewa a nan Baraza gaba daya kaso dari na mazauna yankin suna amfani da itace ne, kuma mun yi wani bincike a nan Baraza mu gane cewa ta yaya suke samun itacen, inda suka ce suna zuwa daji ne su saro itacen, kuma yanzu ma icen na ba su wahalar samu saboda sai sun yi tafiyar awa biyu zuwa uku cikin daji sannan a samo ice, hakan yana iya zama hatsari ga rayuwar matan domin za a iya yi masu fyade a hanya, ko su ji ciwo da dai matsaloli da dama, sai muka lura abun da mazauna garin suka fi yi, inda muka lura cewa suna yin noma sosai kamar Masara, Shinkafa da sauran su, to tun da haka ne ai akwai ragowar albarkatun noman da bayan girbi ana zubar da su ba tare da an yi amfani da su ba, muka tambaye su idan sun yi noman Marasa da Shinkafar ina kuke kai kaikayin da totuwar Masarar sai suka ce zubarwa, muka ce su daina zubarwa za mu koya masu yadda za a yi amfani da su su dawo gawayi domin a rage yawan sare bishiyoyi a daji.”

To ko yaya matan kauyen na Baraza suka ji da wannan shiri? Aishatu Shu’aibu na daga cikin matan da suka amfana.

“Muna sarrafa abubuwan amfanin gona wanda a baya zubar ake yi ba su da amfani amma yanzu an kawo mana ci gaba wanda sarrafa shi muke yi ya zama gawayi, gawayin kuma an yi mana bayani cewa ba shi da illa, yana da kyau ba ya cutar da mata, an kawo mana injina wanda za mu rinka sarrafawa”. (Garba Abdullahi Bagwai)