logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta samar da tallafin kaso 50 ga manoman alkama a kasar.

2023-10-15 15:27:45 CMG HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar dacewa zata bayar da tallafin kaso 50 ga manoman alkama yayin aikin noman rani na bana domin bunkasa samar da abinci a kasa.

Ministan aikin gona Abubakar Kyari ne ya tabbatar da hakan lokacin dayake zantawa da manema labarai a Kano bayan kammala ziyarar wasu cibiyoyin samar da irin alkama domin shukawa a jihar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.