logo

HAUSA

Najeriya da kasar Saudiya za su kara karfafa hadin gwiwa wajen yaki da matsalar sauyin yanayi da ayyukan ta’addanci

2023-10-14 17:23:27 CMG Hausa

Najeriya da kasar Saudiya na duba yiwuwar fadada alakar su ta hanyar hadin gwiwa domin shawo kan kalubalen dake damun su kamar sauyin yanayi, batutuwan da suka jibinci cigaban muradun karni, yaki da ayyukan ta’addanci da masu tsattsauran ra’ayi da kuma bunkasa sha’anin kasuwanci maras shinge.

Karamin ministan harkokin kasashen ketare na kasar Saudiya Adel-Al-Jubeir ne ya tabbatar da hakan bayan wata ganawa ta sirri da shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya ce Najeriya da kasar Saudiya suna magana da murya daya a kungiyar OPEC, sannan kuma suna zama teburi guda a kungiyar kasashe musulmi ta duniya, a don haka alakar su dadaddiya ce.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Karamin ministan harkokin kasashen waje na kasar Saudiya yana tare ne da ministan hakokin kasashen wajen Najeriya Yusuf Tuggar yayin wannan ziyara zuwa fadar shugaban kasa.

Adel-Al-Jubeir ya tabbatar da cewa, kasashen biyu suna da kamanceceniya a bangarori da dama na cigaba, a don haka kara fadada mu’amalar abokantakarsu zai kasance mai fa’idar gaske ta fuskar cigaban tattalin arziki da zamantakewa.

“Dukkannin mu mun yi imani da cewa, kyakkyawar alakar mu za ta ba mu kwarin gwiwar tunkarar kalubalen dake fuskantar wannan duniya tamu, kamar sauyin yanayi ko cigaban muradun karni ko kuma dakile yaduwar ayyukan ta’addanci da kuma masu tsattsauran ra’ayi, haka kuma zai dada baiwa kasashen biyu damar kara daga martaba su zuwa babban matsayi.”

Da yake karin haske game da abubuwan da kasashen biyu suka cimma, ministan harkokin kasashen wajen na Najeriya Alhaji Yusuf Tuggar ya ce,

“Kasancewar dukkanin mu muna samar da albarkatun mai da iskar gas, muna nema wani sabon tsarin amfani da makamashi sabanin yadda muke amfani da shi yanzu, haka kuma kasar ta Saudiya ta bukaci mu kara yin hubbasa wajen kyautata dangantakarmu ta fuskar al’adu.”(Garba Abdullahi Bagwai)